Ko na fadi zaben fidda dan takara a PDP, ba zan fice daga jam’iyyar ba – Bafarawa

0

Tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa ya bayyana wa magoya bayansa cewa shi ba ya irin ‘yan siyasan nan bane da idan basu sami abin da suke so a jam’iyyar da suke ba sai su yi tsalle su koma wata jam’iyyar.

Ya ce ya fito takarar shugabancin Najeriya ne don ya inganta rayukan mutanen kasar nan. Idan ya samu nasara a zaben fidda dan takara, Masha’Allah, idan bai samu ba, zai yi tarayya da wannda ya samu nasara domin ganin jam’iyyar ta kai ga ci a 2019.

” Wasu sun tsallako zuwa PDP ne domin su yi takarar kujera, ba wai don suna so jam’iyyar ta ci gaba ba.

Shugaban Jam’iyyar PDP a jihar Sokoto, Tanko Bege ya yaba wa tsohon gwamna Bafarawa sannan ya yi masa fatan alkhairi bisa ga abin da ya sa a gaba.

Sauran ‘yan takaran sun hada da Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Makarfi, Gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, tsohon Mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar, Aminu Tambuwal, Sule Lamido, Kabiru Turaki da dai sauran su.

Share.

game da Author