PDP ta yi watsi da sakamakon zaben cike-gurbin Sanatan Bauchi

0

Jam’iyyar PDP ta yi watsi da sakamakon zaben cike-gurbi na sanatan Bauchi ta Kudu, wanda Yahaya Gumau na jam’iyyar APC ya yi nasara.

PDP ta bayyana cewa ba ta yi na’am da sakamakon da aka bayyana ba, ta na mai zargin cewa an tabka magudi.

INEC ta bayyana Gumau a matsayin wanda ya yi nasara da yawan kuri’u 119,489.

Dan takarar jam’iyyar PDP, Ladan Salihu, kuwa shi ya zo na biyu da kuri’u 50,256.

Gumau dama shi ne dan majalisar tarayya mai ci a yanzu, ya yi nasara ne a zaben da aka yi a kananan hukumomi bakwai na shiyyar ta Bauchi ta Kudu, yayin da Salihu ya samu karamar hukuma daya kawai.

Yawancin wakilan hukumar zabe da ke kananan hukumomi, sun aika da rahoton harkalla a wurin zaben, sannan kuma an soke kuri’u har kusan 60,000 a rumfunan zabe daban-daban na shiyyar da aka gudanar da zaben.

PDP ta ce tun da aka kafa jihar Bauchi ba a taba tabka magudi kamar irin wanda aka yi a wannan lokacin a zaben cike-gurbi a jihar Bauchi ba.

Jam’iyyar kuma ta ce an yi hadin-baki tsakanin jami’an zabe, jami’an tsaro da kuma gwamnatin jiha domin a yi magudi.

Sai dai kuma wasu kungiyoyi sun ce an yi zaben lami lafiya.

Share.

game da Author