Wasu likitoci da suka kware a wajen kula da masu fama da ciwon Farfadiyya a kasar Australia sun gano cewa Wiwi na warkar da masu fama da ciwon farfadiya.
Shugaban likitocin John Lawson ya bayyana haka ranar Litini inda ya kara da cewa sun gano haka ne a wani bincike da suka gudanar a jikin wasu yara dake fama da wannan ciwo su 40.
” Da muka gwada yin amfani da ganyen a jikin yaran sai kusan rabi daga cikin su suka warke, sauran da basu warke ba kuma suka sami saukin gaske daga ciwon.
Lawson ya ce duk da cewa binciken da suka gudanar ya samar musu da sakamako mai kyau, yayi ira da aci gaba da yin gwaji a akai domin samun nasara a kai mai nagarta.
A karshe ya kuma yi kira ga gwamnati da ta kafa matakan da za su hana iyaye da mutanen da suke fama da wannan cutar yin amfani da tabar wiwi kai tsaye domin yin haka na tattare da matsala
Sannan ya yi kira ga gwamnatocin kasashe da su gaggauta sarrafa wannan magani domin hakan zai taimaka wajen hana mutane yin amfani da ganyen itacen kai tsaye.
Discussion about this post