Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ta kama wasu mutane 8 da ta yi zargin yunkurin kai hari a kasuwar kauyen Gurbin Baure, da ke cikin Karamar Hukumar Zurmi, cikin Jihar Zamfara.
Kakakin ‘yan sandan jihar, Shehu Mohammed ya ce an cafke su ne bayan da wani ya yi jami’an tsaro kiran gaggawa, yace mahara na can da niyyar kai farmaki a kasuwar ta Gurbin Baure.
Ya ce da ya ke sun je cikin gaggawa, sun same su har sun yi garkuwa da wani mutum mai suna Jafar Yusuf.
Ya ce nan da nan ‘yan sanda suka kewaye wuri, kuma suka ceci wanda aka yi garkuwar da shi, wanda tuni kafin ‘yan sanda su kai wurin har ya ji ciwo. Mun kama mahara 8, an samu bindigogi kirar gargajiya da kuma wuka biyu
Daga nan ya ce da zaran an gama yi wa wadanda ake tuhumar tambayoyi, za a gaggauta gurfanar da su a gaban shari’a.