Sojojin da ke yaki da Boko Haram sun yi bore, sun kwace filin jirgin sama na awa biyu

0

Hukumomin Tsaron Sojojin Najeriya sun tabbatar da cewa sun kwantar da hargitsin da ya tashi a filin jirgin saman Maiduguri, bayan da wasu sojoji da ke zanga-zanga suka kwace filin jirgin na tsawon awa biyu a jiya Lahadi.

Wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na sojojin Operation Lafiya Dole, Onyema Nwachukwu, ya bayyana abin da sojojin suka yi da cewa abin yi wa tir ne matuka.

Ya ce hargitsin ya tashi ne a filin jirgin saman Maiduguri, bayan da aka bada umarnin sauya sojojin da ke tsaro na cikin Maiduguri da nufin kara tsaurara tsaro a cikin birnin.

“Sauya sojoji a maye gurbin su da wasu ya zama wajibi, bayan wani bin-diddigi da aka gudanar. Amma abin takaici, sai wasu tsirarun sojoji su ka yi wa sauyin mummunar fahimta, su ka dauka cewa sauyin da za a yin musu zai shafi lokacin wa’adin su na zama Maiduguri. Wannan ne ya harzuka su har suka fara harbe-harbe a sama.

“Amma dai an kwantar da tarzomar, domin Babban Kwamandan Lafiya Dole, Manjo Janar Abbas Dikko, ya gaggauta shawo kan lamarin.

“Rundunar Gangamin Yaki da Boko Haram ta dauki wannan bore da suka yi a matsayin abin takaici da kuma da-na-sani, kuma ba daidai ba ne. Ana kokarin daukar matakin da zai hana sake faruwar irin wannan.

Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa hasalallun sojojin sun tada bore ne, bayan ikirarin da suka yi cewa lokacin da ya kamata a maida su bariki ya wuce, to dalili kenan su ka yi tawayen kin amincewa a tura su garin Marte, daya daga cikin garuruwan da aka kwato daga Boko Haram shekarun baya.

Sojojin da suka yi boren na daga cikin zaratan da aka girke a Filin Jirgin Maiduguri domin kara tabbatar da tsaro.

Masu boren sun tare wani sashe na filin jirgin, suka rika harba bindigogi sama. Wannan al’amari ya firgita dandazon maniyyatan da ke filin da ke jira jirgi ya dauke su zuwa Saudiyya, suka fantsama a guje, kowa ya yi ta kan sa.

Wani soja da baya so a ambaci sunan sa, ya ce kokarin sauya musu wurin aiki ya saba da umarnin Hedikwatar Tsaro ta Kasa.

“Sojojin da aka girke a filin jirgin wadanda aka yi niyyar daukewa a kai su Marte, ba su da cikakken horo batakashi a yakin kasa. An yi musu horo ne na bayar da kariya wajen kare hare-hare daga sama.

“Mu aikin mu shi ne bayar da kariya daga hare-haren sama. Wadanda aka yi wa irin horon yakin kasa, su na can Maiduguri an girke. Amma abin haushi wai sai aka ce an maida mu zuwa Marte, inda za mu kai kanmu a kashe mu.

Wani sojan kuma korafin sa shi ne sun dade, tuni ya kamata a ce an janye su, an kawo wasu.

Ya ce da yawa daga cikin su sun kwashe shekaru uku su na fafata yaki.

Share.

game da Author