Ka dawo gida, ba mu yin ka tun da ka fice daga APC – Mutanen Hadejia ga Sanata Ubale

0

Mutanen garin Hadejia sun yi zangar- zangar nuna kiyayyar su kuru-kuru ga sanatan da ke wakiltar Jigawa ta Arewa, Ubale Shittu.

Matasan na kira ne ga sanata Ubale Shittu da ya sauka daga kujerar sanata da yake a kai.

Babban Laifin sa shine komawa jam’iyyar PDP da ya yi daga APC.

Wadannan matasa sun tako ne wasu da kafa wasu bisa ababen hawa, tun daga masana’antar sarrafa rake dake Hadejia zawa fadar sarkin Hadejia a na kwarara ruwan sama suna raira wakoki suna cewa ‘duk wanda ya ki Buhari barawo ne’,‘Buhari shi ne mai cecen mu daga nan har 2023.’

Tun kafin Shittu ya fice daga APC ba su shiri dama da gwamnan jihar Mohammed Badaru. Ya sha yin barazana sai ya tsige gwamna Badaru daga kujerar gwamnan jihar Jigawa.

Daya daga cikin masu fada a ji a jam’iyyar APC a jihar Bala Umar ya bayyana wa manema labarai cewa Shittu ya yanke hukuncin ficewa daga APC ne ba tare da ya yi shawara da mutanen mazabar sa ba da haka ya sa suka yi masa bore.

” Yanzu haka sanata Ubale a boye yake shigowa garin Hadejia kamar mara gaskiya.

Share.

game da Author