Babu alamu Majalisar Tarayya za ta dawo gobe Talata

0

Kwana daya kacal kafin komawar gaggawa da Majalisar Tarayya ta bayyana cewa za ta yi gobe Talata, domin zama kan muhimman batutuwan kasa, har zuwa yau an kasa tabbatar da cewa ko majalisar za ta zauna gobe.

Dama dai Mataimakin Shugaban Majalisar Tarayya ne, Yusuf Lasun, a cikin makon da ya gabata yace mamabobin majalisar za su koma a ranar Talata mai zuwa domin tattauna batutuwa masu muhimmanci.

Ana sa ran idan aka koma, za a tattauna batun amincewa da kasafin kudin da za a kashe wajen gudanar da zaben 2019, wanda ke da bukatar amincewa ta gaggawa. Domin hakan ne zai sa hukumar maida hankali wajen ci gaba da shirya zaben.

Sai dai kuma, da PREMIUM TIMES ta tuntubi kakakin yada labaran Kakakin Majalisar Tarayya, Turaki Hassan, ya ce idan majalisa za ta koma aiki, to sai an fara samun sanarwa daga babban mai kula da harkokin majalisa, wato ‘clerk.’

“To kuma har yanzu da na ke magana da kai, babu wata sanarwar da ta zo mana daga ofishin sa.”

Ya ce da wuya majalisa ta zauna a ranar Talata, sai fa idan kafin nan da karshen wannan rana ta Litinin sun samu sanarwa ko wasika daga ofishin babban jami’in majalisar.

Hon. Nicholas Ossai daga jihar Delta, ya bayyana cewa shi ba shi da ma labarin cewa za a koma ranar Talata din.

Ya ce idan har za a yi irin wannan komawar, to sai an sanar da shugabannin majalisar tukunna.

Share.

game da Author