Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya zargi limaman Kiristoci da kauda kai daga yi wa jama’a wa’azi game da illar cin hanci da rashawa.
Osinbajo ya ce fastocin ba su taimaka wa Gwamnatin Tarayya wajen kokarin da ta ke yi na kawar da rashawa da cin hanci.
Da ya ke magana a taron Kungiyar Dalibai Kiristoci karo na 30 a garin Enugu, Osinbajo ya yi tsokacin cewa limaman kiristocin wannan zamani sun fi karkata wajen yi wa mutane addu’ar yadda za su yi arzikin dare-daya-daya-Allah-ka-yi-Bature.
“Da wuya ka ji irin wadannan masu wa’azin su na magana a kan illar cin hanci da rashawa idan su na kan mimbari. To ya kamata dai su sani cewa idan kasa ba ta kan turba madaidaiciya, to babu abin da zai iya wakana na daidai a cikin ta.”
Ya ce matsalar Najeriya ba kabilanci ko addinanci, ba ne, sai dai kawai cin hanci da rashawa.
Ya kara da cewa matsalar wawurar kudi ta yi wa Najeriya katutu, har abin ya kai idan ka ce z aka yi yaki da ita, to zai ne za ka koma maras rinjayi a cikin al’umma.
Daga nan sai ya kalubalanci matasa da su tashi tsaye wajen yaki da karfa-karfar da wadanda suka wawure kudaden kasa ke yi musu.