Kauyen Jarkasa da ke cikin karamar Hukumar Igabi cikin jihar Kaduna, ya hargitse a jiya Asabar, bayan da wasu mahara su ka yi wa ‘yan sanda hudu kisan kwanton-bauna.
Kisan ya faru ne da safiyar Asabar yayin da ‘yan sandan suka shiga cikin dajin Jarkasa, domin su fatattaki mahara.
Dama an samu rahoton cewa akwai mahara a cikin kauyen.
An ce an tura ‘yan sandan ne daga cikin Zaratan Farmakin Gaggawa na ‘Yan sanda daga Abuja.
Wani manomi a Rigasa, wanda gonar sa ke kan hanyar shiga dajin, ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa an rika jin tashin rugugin karar bindigogi a lokacin da ake yakin.
” Ina kan hanyar zuwa gona, sai muka rika jin karar bindigogi. Kuma sai muka rika ganin hayaki na fitowa daga cikin wata matsugunar Fulani da ke kusa da gonar.” Haka wannan manomi mai suna Aliyu ya bayyana wa PREMIUM TIMES.
“Sannan na ji labarin cewa an kashe ‘yan sanda hudu. Amma sai na yanke shawarar cewa ba zan karasa gona ta a ranar ba, tunda ban san abin da zai biyo baya ba.’’
“PREMIUM TIMES ta samu labarin cewa mazauna garin Rigasa sun rika yin tururuwar fita su na kallon wasu matan Fulani na ficewa daga cikin dajin bayan an gama gumurzun.
“Jami’an tsaro sun banka wa bukkokin su wuta, sannan hayaki ya turare sama yayin da ake ganin matan na ficewa daga cikin dajin. Haka wani mai suna Anas ya bayyana.
Kakakin Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Kaduna ya tabbatar da afkuwar kisan.
PREMIUM TIMES ta bayar da labarin yadda aka yi garkuwa da malamin nan na Kaduna, Sheik Algarkawy a cikin dajin.
An ce sai da aka biya diyya sannan aka sake shi.