‘Yan sanda a Lokoja, Babban Birnin jihar Kogi, sun tabbatar da kashe mutum biyu yayin gudanar da zaben cike-gurbin dan Majalisar Tarayya na Lokaja da Kogi.
Kakakin ‘yan sandan, William Aya, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN cewa mutane biyu ne aka kashe.
Ya ce an kashe Yadau Umoru a Unguwan Pawa Kofar Fadar Maigari, a lokacin da yayi kokarin satar akwatin zabe.
Ya ce yanzu haka ana ajiye da gawar mamacin a dakin adana gawarwaki da ke Asibitin Tarayya na Lokoja.
Dama kuma wani mutum da ba a gane ko wane ne ba, shi ma ya rasa ran sa a jiya Asabar din kafin kisan da aka yi wa Umoru.
An kashe wanda ba a fayyace ko wane ne ba a mazabar ofishin kamfanin raba hasken lantarki, AEDC, a Lokoja, shi ma a kokarin sa na satar akwatin zabe.
Kamfanin Dillancin Labarai, NAN ya ruwaito cewa an fara zaben lafiya kalau, amma daga baya sai ya rikide zuwa dandalolin hada-hadar cinikin kuri’u.
Discussion about this post