HAJJI 2018: Wata mata ta gano kudin guzirin ta da ya bace a cikin wani otal

0

Wani mahajjaciya tayi sa’ar gano kudin guzirin ta har dalar Amurka 700 da suka bace a otal din da ta sauka.

Hassana Aliyu, daga Karamar Hukumar Gezawa Jihar Kano, ta batar da kudin ta, amma sai wani ma’aikacin otal din ya tsinci kudin, kuma nan take ya damka su ga jami’an kula da otel din mai suna Al-Andalus Al-Masi, da ke tsakiyar Madina.

Hassana ta gode wa masu otal din, kuma ta yaba wa jami’in NAHCON, Umar Bala.

Shi ma wani mahajjaci da ga jihar Nasarawa ya gano kudin sa dala 600 a otal din da Hassana ta jefar da na ta kudin.

NAHCON ta ce zuwa yanzu ta yi jigilar maniyyata har 26,697.

Share.

game da Author