Hukumar Yaki da Cin Hanci, Rashawa da Hana Laifukan Zamba(EFCC), ta maida wa mashawarcin Shugaba Muhammadu Buhari kan Harkokin Siyasa, Babafemi Ujudu cewa ba ta da wata alaka da Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki.
Ujudu ya yi wannan zargin ne a cikin wani rubutu da ya fi kwanan nan.
An rika yin wannan cikin daga cikin makon da ya gabata cewa wasu jami’an tsaro na aiki tare da Saraki, domin yi wa dimokradiyya ko wannan gwamnati zagon-kasa.
Wannan ya biyo bayan mamayar da jami’an SSS suka yi wa Majalisar Tarayya ne, wanda wasu ke zargin cewa da hadin bakin SSS da Saraki aka kai harin.
Sai dai kuma Saraki ya fito ya karyata haka, har ya kara da cewa wanda ya fadi hakan to ya raina wa ‘yan Najeriya hankali.
Hukumar EFCC ta bakin kakakin ta, Wilson Awujeren, ta ce zargin da Ujudu ya yi a matsayin sa na mashawarcin shugaban kasa, ba gaskiya ba ne, kuma abin takaici da mamaki ne.
Ya ce ya kamata kowa ya yi watsi da rubutun na Ujudu, tare da yin kira ga ‘yan siyasa su rika tuntuba sun a tantance batutuwa kafin su kai alkalamin su kan takarda, ko kuma kafin su yi wani furucin da bai dace ba.