Ahmad Babba-Kaita na Jam’iyyar APC ya lashe zaben Sanata a Katsina

0

Dan takarar kujerar Sanata na jam’iyyar APC, Ahmad Babba-Kaita ya lashe zaben cike gurbi da aka gudanar ranara Asabar a Katsina.

Kamar yadda aka bayyana sakamakon, Ahmad Babba-Kaita ya sami kuri’u 224,607 sannan Wan sa, da tsohon ma’aikacin kwastam ne, kuma dan takara na jam’iyyar PDP Kabir Babba-Kaita ya sami kuri’u 59,724.

Hukumar Zabe mai zaman kanta ta bayyana cewa cikin mutane 855,092 da suka yi rijista, sama da mutane 300,000 ne aka tantance a rumfunar zabe dake wannan shiyya.

Share.

game da Author