Wata budurwa, Ramlatu ta guntule azzakarin saurayin ta a Jigawa

0

Kakakin rundunar tsaro na ‘Civil Defence’ na jihar Jigawa Adamu Shehu ya bayyana wa manema labarai cewa wata budurwa mai suna Ramlatu Tafida, mai shekaru 17 ta guntile azzakarin saurayin ta Abdullahi Sabo.

Wannan mummunar abu ya faru ne a karamar hukumar Babura, jihar Jigawa.

Ramlatu ta sanar wa jami’an tsaro cewa sun gama shiri tsaf da Abdullahi za su yi aure domin ma har ya aika da kudin gaisuwa naira 30,000 gidan su.

” Bayan haka sai muka zo muka shaku da har saduwa mukan yi akai-akai da Abdullahi. Ana nan ana nan sai naji wai Abdullahi na kokarin yin watsi da ni ya auri wata yarinyar dabam.

” Da na ji haka sai na boye wuka ta a jiki na wata rana da muke tare a daki zamu sadu da juna bayan muna gab da mu fara sai ko na ciro wukar na yanke masa azzakari.

Abdullahi dai malamin makarantar sakandare ne dake karamar hukumar Babura, jihar Jigawa, kuma dan shekara 25.

Adamu Shehu ya ce wani mutumin kirki ne ya rugo ofishin su ya gaya musu cewa ga wasu matasa can za su yi ma wata yarinya dukan tsiya.

” Daga nan ne muka aika jami’an mu suka je suka shawo kan alamarin.

Ita dai Ramlatu ta ruga gidan su ne bayan ta aikata wannan abu ta shida wa mahaifiyar ta.

Yanzu dai an garzaya da Abdullahi asibitin Aminu Kano, ita kuma Ramlatu na tsare a ofishin ‘yan sanda.

Share.

game da Author