Zan matsa a gyara kundin tsarin mulkin kasa da zai sa Buhari ya ci gaba da mulki har rai – Gumau

0

Dan takarar sanata a jam’iyyar APC na Bauchi ta Kudu Lawal Gumau ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa yake so ya tafi majalisar dattawa shine don ya ga shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ci gaba da mulki har ran sa.

Gumau ya fadi haka ne a taron kamfen din sa da yayi a Bauchi Kafin.

Ya ce Buhari ya cancanci ya ci gaba da mulki ne har ran sa kuma abin da zai sa a gaba kenan idan ya sami nasarar lashe zaben kujerar Sanata da ake yi yau Asabar shiyyar.

Tsohon Babban Darektan gidan Radiyon Tarayya, Ladan Salihu na jam’iyyar PDP ne dan takarar da ake ganin zai iya taka masa burki a wannan zabe.

Sai dai kuma duk da haka akwai tsohon gwamna Isah Yuguda da shima dan takara ne na kujerar sanata din a Jam’iyyar GNP.

Share.

game da Author