Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta sanar da kafa dokar hana walwala a kananan hukumomi bakwai a jihar.
Kakakin rundunar Kamal Abubakar ya sanar da haka ranar Alhamis.
Ya ce an yi haka ne domin a samu gudanar da zaben cike gurbin Bauch ta Kudu da za a yi ranar Asabar.
Abubakar yace dokar za ta fara aiki ne daga ranar Juma’a 10 ga watan Agusta daga karfe 12 na dare zuwa karfe takwas sannan a ci gaba washe gari 11 ga watan Agusta.
” Kananan hukumomin da wannan dokar ya shafa sun hada da Bauchi, Toro, Alkaleri, Bogoro, Tafawa Balewa, Dass da Kirfi.
” Mun kafa wannan dokar ne bayan tattaunawa da muka yi da masu ruwa da tsaki a jihar.”
A karshe jami’in hukumar zabe na jihar Ibrahim Abdullahi ya yi kira ga duk jam’iyyun da su gaya wa magoya bayan su da su bi doka a loka in zabe.