TAMBAYA: A bani gajeruwar tarihin mutumin nan da yayi tafiya da Annabi Musa a suratul Kahfi, Annabi ne?

0

TAMBAYA: A bani gajeruwar tarihin mutumin nan da yayi tafiya da Annabi Musa a suratul Kahfi, Annabi ne? Tare da Imam Bello Mai-Iyali

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Khidir shine mutum da yayi tafiya da annabi Musa Alaihis-Salam Allah ta’ala ya ambaci kissarsa a suratul kahfi cikin Al’kur’ani, amma ba a ambaci sunansa ba, kuma yadda addinin Kiristanci da Yahudanci sun rabarto kissasa.

An samu sabani mai yawa da ruwayoyi daban-daban a tarihinsa. Tarihin da malaman Musulunci suka ruwaito ya saba da na sauran marubuta tarihi. Suma malaman musulunci sun samu sabani acikin wasu abubuwa.

Wannan bawan Allah shi ne Halliru dan Adamu a hausance, a larabce kuwa ana kiransa da Khidir Ibn Adam Alaihis-Salam. Shi da ne na cikin Adamu da Hauwa’u, Allah yayi masa tsawon rai albakacin addu’ar babanmu Annabi Adamu Alaihis-Salam. Sakamakon wasicin da Annabi Adamu Alaihis-Salam yayi wa ‘ya’yansa cewa idan ruwan dufana ya zo, su cire gawarsa su rufeshi awani guri na musamman, kuma yayi addu’ar tsawon rai ga wanda ya cika wannan Wasici. An ruwaito cewa Khadir ne ya cika
wannan umurni na Annabi Adamu Alaihis-Salam.

Duk dacewa wasu malamai suna cewa ya mutu, ammafa wasu ruwayoyi daga wasu manyan malamai suna tabbatar da cewa yanada rai har gobe, kuma ba zai mutu ba sai karshen duniya.

Malamai sunyi sabani akan cewa, shin annabi ne shi ko waliyyi ne daga cikin bayin Allah Salihai? Khidir Annabi ne daga cikin annabwan Allah, ta dalilin fadin Allah a cikin suratul Kahfi, sai Khadir Alaihis-Salam ya cewa Annabi Musa Alaihis-Salam: duk abinda ka gani na ilimi da ban
mamaki ba nayi bane da umurnin kaina ba. Duk wanda Allah ya umurta kai tsayi, to ya zama annabi.

(Allah shi ne mafi sani).

Share.

game da Author