Wasu likitoci a jami’ar ‘Central Queensland’ dake Australia sun gano cewa za a iya amfani da kashin kada wajen warkar da masu fama da cututtukan da ya shafi kashin jikin mutum.
Jagoran wadannan likitoci ‘Padraig Strappe’ ya bayyana cewa sun gano haka ne a binciken da suka yi da gwajin kasusuwan kada da amfanin su.
Strappe ya ce sakamokon da suka samu daga wannan bincike ya nuna cewa kasusuwan kada na na iya warkar da cututtukan da ke kama kashi kamar su ciwon kafa wato ‘Arthritis’da raunikan da ake samu a mahadan kashi dake jikin mutum.
Strappe ya ce kasusuwan da ke da amfani a jikin mutum sune kasusuwar hakarkari da wanda ke bindi.
A karshe y ace wadannan kasusuwan sun fi inganci ne saboda su ne suka fi daukan bangaren jikin kada da ke da nauyi