A yau Alhamis ne cibiyar bincike da hidimomi (DRPC) shirya taron domin samar da hanyoyin bunkasa yin alluran rigakafi a kasar nan.
Cibiyar DRPC ta shirya wannan taron da aka yi a Abuja tare da hadin guiwar kungiyar ma’aikatan kiwon lafiya na kasa (NACHPN).
Jami’in cibiyar DRPC Hassan Karofi ya ce wannan taron ya sami goyan bayan gidauniyar Bill da Melinda Gates na kasar Amurka.
A bayanan da ya yi Karofi ya ce Najeriya za ta iya bunkasa kiwon lafiyar mutanen ta ne idan ta karfafa hanyoyin wayar da kan mutane game da mahimmancin yi wa ‘ya’yan su allurar rigakafi tare da bada bayanan aiyukkan da take yi.
” Wadannan dabaru biyu na cikin hanyoyin da za su taimaka wa kasar wurin hanzarta karfafa yin allurar rigakafi da aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da ake da burin ganin an sami nasara akai daga 2018 zuwa 2028.”
A karshe Karofi ya ce kungiyar NACHPN za ta jagoranci zantar da wadannan dabaru da suka tattauna a kai a jihohin Kano, Kaduna, Neja da Legas.
Ma’aikatan fannin kiwon lafiya da kungiyoyin bada tallafi kan yin allurar rigakafi da dama sun halarci wannan taro da aka yi wanda a cikin su akwai shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko Faisal Shuaib da jami’in kungiyar dRPC-PACFaH@Scale, Emmanuel Abanida da dai sauran su.
Discussion about this post