Jagorar jam’iyyar APC Bola Tinubu ya bayyana cewa dukkan su suna sane da tuggun da ake kitsawa don a tsige shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Tinubu ya fasa kwan ne a gari Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom, inda ya kara da yin garadi ga masu yin wannan shiri da su mai da hankalin su kuma su sani cewa kadangare ba zai iya kokuwa da gada ba.
” Najeriya kasar mu ne kuma kasa ce domin mutanen Najeriya. Duk abin da za muyi muna yi ne don Najeriya da ‘yan Najeriya. Buhari ya ce dole mu canza, a daina satar kudin gwamnati, ayi wa talakawa aiki, shine ya sa wasu ke ganin ba haka ba.
” Sun fi so aci gaba da watandar kudaden gwamnati wasu kadan na wawushe su.” Inji Tinubu
Shiko Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha cewa yayi gwamnatin Buhari gwamnati ce da take tafiya da kowa da kowa.
” Akwai ministoci 38 a kasar na, 18 musulmai, 18 Kirista. Kuma ina so a sani cewa Kiristoci ne suka fi rike manyan ma’aikatu a kasar nan. Sannan kuma ga irin su ofishin gwamnan babban bankin Kasa, da kuma na sakataren gwamnatin tarayya.
A yau ne dandazon magoya bayan tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom Godswill Akpabio suka hallar babban filin wasa ta jihar domin yi wa tsohon gwamnan maraba da shiga jam’iyyar APC daga PDP.
A dalilin haka gwamnan jihar Emmanuel Odom ya kori wasu daga cikin kwamishinonin sa biyu da suka halarci filin taron domin taya Akpabio Murna.