HAJJI 2018: An fara jigilar maniyyata daga jihar Legas

0

Kwamishinan ayyukkan cikin gida na jihar Legas Abdulhakeem Abdullateef ya bayyana cewa jihar ta fara jigilar maniyyata daga jihar zuwa kasar Saudiya domin aikin hajjin bana.

Abdullateef ya fadi haka ne ranar Laraba da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Legas.

Ya ce bana maniyyata 2000 ne suka yi rajistan tafiya aikin hajjin bana da hukumar Alhazai ta jihar.

” A yanzu dai mun fara jigilar mutane 1273 daga cikin 2000 din da suka yi rajista sannan za mu ci gaba da jigilar wadanda suka rage daga ranar Juma’a.”

Abdullateef ya yi kira ga maniyyatan jihar da su kiyaye sharuddan aikin hajji yayin da suke kasar Saudi.

A karshe yace gwamnatin jihar Legas za ta kammala shirye-shiryen da ya kamata don ganin mahajjatan jihar sun yi aiki lafiya sun dawo kasa Najeriya lafiya.

Share.

game da Author