Jami’in hulda da jama’a na hukumar jindadin Alhazai ta jihar Kaduna Yunusa Abdullahi ya bayyana cewa hukumar ta yi jigilar maniyyata sama da 2000 zuwa yanzu daga jihar Kaduna zuwa kasa mai tsarki.
Abdullahi ya bayyana cewa bayan wadanda aka riga aka tafi da su daga jihar Kaduna kasar Saudiyya zuwa yanzu, za a ci gaba da aikin jigilar sauran da suka rage.
” Kamfanonin jiragen sama na Med-View da Max Air ne suka kwashi maniyyata da aka riga aka yi jigilar su zuwa kasar saudiyya din domin aikin hajji.” Inji Abdullahi.