Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki, ya bayyana cewa ba zai biye wa masu kiraye-kirayen cewa ya sauka daga shugabancin majalisar ba.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke bayani ga dandazon manema labarai a Majalisar Tarayya, a yau Laraba.
Tun daga lokacin da Saraki ya bayyana ficewa daga APC zuwa PDP, sai jam’iyya mai mulki ta rasa rinjaye a majalisar.
A yau Saraki ya bayyana cewa ba zai sauka daga shugabancin majalisa ba, matsawar abokakn aikin sa mambobin majalisa da suka zabe shi sun a bayan sa.
“Ba zan bi abin da masu matsa min lamba ke so na yi ba, wato na sauka. E, ba zan sauka din ba, domin mambobin majalisar dattawa ne suka zabe ni.”
Saraki ya ci gaba da cewa ba mulki ya ke kwadayi bakin rai bakin fama ba. Kuma da zaran wadanda suka zabe shi sun ce ba su son sa, to nan da nan zai sauka.
Saraki ya kara da cewa idan kashi biyu bisa uku na ‘yan majalisa suka ce ba su bukatar sa, sauka zai yi ba da wani bata lokaci ba.
Daga nan sai ya yi kira ga ‘yan Najeriya su yi watsi da surutan masu cewa wai shi tsananin kwadayin mulki gare shi.
A lokacin da ake wannan taron manema labarai, Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara na zaune a gefen sa.
Saraki ya kara da cewa shi ma Yakubu Dogara sauka zai yi idan mafi yawan mambobin majalisar tarayya suka ce ba su bukatar sa.