Idan ba a manta ba, a ranar Talata ne mmukaddashin shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya kori shugaban hukumar SSS, Lawal Daura daga shugabancin hukumar.
Babban makasudin yin haka shine, yadda yayi gaban kan sa wajen aika jami’an hukumar majalisar kasa, inda aka ci mutuncin wasu daga cikin ‘yan majalisar da suka halarci majalisa a ranar Talata.
A bincike da muka gudanar, ya nuna cewa ashe tafka rashin mutunci ne Lawal Daura ya yi wa mukaddashin shugaban Kasa Yemi Osinbajo.
” Bayan Yemi ya bukaci Lawal Daura ya bayyana a ofishin sa bayan jin abin da jami’an hukumar sa suke yi majalisar kasa.
Shigowar Lawal Daura ke da wuya sai Osinbajo ya nemi yayi misa bayanin ko wanene ya bashi umarnin aikawa da jami’an sa majalisar Kasa. Shi ko gogan naka da bude bakin sa sai ya ce shi ba ya aiki da umarnin Mukaddashin Shugaban Kasa, Buhari ne ya nada shi kuma shi ne ya ke da iko a akan sa ba Osinbajo ba.
Daga nan sai Osinbajo ya umurni Kakakin sa ya sanar da korar sa a matsayin shugaban hukumar SSS din, sannan a tsare shi tukuna.
Daga baya sai aka dauke shi dungurungun zuwa ofishin rundunar SARS dake Abuja inda har yanzu yana tsare.
A rashin sani na Lawal Daura, ashe shi kan sa Osinbajo, sai da ya tattauna da shugaba Buhari kafin ya aika a kira Lawal Daura.
Discussion about this post