Mazaunin gidan haya ya maka maigida a kotu saboda ci masa mutunci da ya yi

0

Ofishin ‘yan sandan dake Durumi Abuja ta gurfanar da wani mai gidan haya Sunday Agbo a kotu dake Wuse Zone 6 Abuja kan zargin sa da cin mutuncin wani mazaunin gidan sa na haya.

Lauyan da ya shigar da karar, Fidelis Ogbobe ya bayyana cewa Bako Abubakar da ke haya a gidan hayan Sunday dake Plot 692 a Durumi a Abuja ya shigar da kara a ofishin ‘yan sandan Durumi ranar 13 ga watan Afrilu cewa magidan hayan sa ya hana shi da iyalen sa zama a gidan da suke haya sannan har ya bada wani bangaren gidan haya wa wata coci.

Fidelis ya bayyana cewa Sunday ya garke gidan da Bako ke zama sannan ya sa jami’an tsaro gadin wurin domin hana Bako da iyalen sa shiga gidan.

Shi kuwa Sunday ya musanta aikata haka a gaban alkali da kotu.

A karshe alkalin kotun Abdulmajid Oniyangi ya bada belin Sunday kan Naira 250,000 tare da gabatar da shaidu biyu.

Za a ci gaba da shari’ar ranar 3 ga watan Satumba.

Share.

game da Author