Osinbajo ya kori Lawal Daura

0

Mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya fatattaki shugaban hukumar DSS Lawal Daura.

A wasikar sallamar da aka mika masa, an umurce shi da ya mika ragamar mulkin ga babban darekta a ke hukumar.

Wannan kora da aka yi wa Lawal Daura dai ya na da nasaba yadda jami’an tsaro na DSS suka far wa majalisar kasa da safiyar Talata.

Kafin a kori Lawal Daura sai da mataimakin shugaban Kasa ya umarce shi da sufeto janar su bayyana a ofishin sa.

Jim kadan bayan sun bayyana ne fa Osinbajo ya fatattake shi.

Share.

game da Author