Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya sauka daga mukamin sa. Hakan ya biyo bayan komawar sa jam’iyyar APC daga PDP.
A cikin wata wasika da ya aika wa Sanata Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye, Emmanuel Bwacha, Akpabio ya ce ya sauka tun daga ranar 4 Ga Agusta, 2018.
Ya gode wa shugabannin majalisar ta dattawa da har suka ba shi damar shugabancin marasa rinjaye na tsawon shekaru uku da ya yi.
Akpabio, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, ya garzaya Landan inda Shugaba Muhammadu Buhari ke zaman hutu ya je ya yi mubayi’ar komawa jam’iyyar APC daga PDP.
Bayan dawowar sa Najeriya kuma, Akpabio ya ziyarci jagoran APC, Bola Ahmed Tinubu.
Ana sa ran yin gangamin karbar sa a Ikot Ekpene, da ke Akwa Igbom.
Ya shiga APC dauke da shirgin nauyin zargin harkallar danne wasu biliyoyin kudade.
Hawan Buhari mulki ke da wuya a cikin 2015, Akpabio na daya daga cikin wadanda yaki da cin hanci da wawurar kudade ya fara yi wa dirar mikiya.
Discussion about this post