Shugaban hukumar kula da hana yaduwar cututtuka na kasa (NCDC) Chikwe Ihekweazu ya bayyana cewa Najeriya za ta bukaci Naira biliyan hudu domin hana bullowar cututtuka a kasar.
Ya fadi haka ne a taron tsara hanyoyin hana bullowar cututtuka a kasar da aka yi a jihar Legas a makon da ta gabata.
Ihekweazu ya ce sun shirya wannan taro ne domin hada kawance da kungiyoyin masu saman kan su domin dakile yaduwar cututtuka a kasar nan.
” A lokacin da cututtukan bakon dauro,sankarau, kwalara, monkey pox da sauran su suka bullo hukumar NCDC ta taka mahimmiyyar rawa wajen ganin an dakike yaduwar cututtukan.
Ihekweazu yace idan ana bukatan a sami sakamako na dindindin sai fa an ware Naira biliyan 4 domin haka.
” Sai dai gwamnati baza ta yi yin haka ba ita kadai musamman yadda kungiyoyi masu zaman kanzu ke da mahimmiyar rawa da za su iya takawa don samar wa mutanen kasar kiwon lafiya ta gari.
” A yanzu dai hukumar na kokarin tsaro hanyoyin da za su fi dacewa domin ganin hakan ya faru musamman yadda babu wanda ke da masaninyar randa wata cutar za ta sake iya bullo.
Discussion about this post