NHIS ta dakatar da asibitoci hudu daga shirin inshorar Lafiya a jihar Bauchi

0

Jami’in hukumar shirin inshorar lafiya ta kasa (NHIS) Sani Affa ya sanar cewa hukumar ta dakatar da wasu asibitoci hudu daga ci gaba da shiri a jihar Bauchi.

Affa ya bayyana cewa hukumar ta yi haka ne a dalilin sabawa dokokin hukumar da wadannan asibitoci suka yi.

Affa yace wadannan asibitoci da suka dakatar sun hada da asibitin Abubakar Tafawa Balewa, people’s clinic Ltd, Alwadata Consultants Hospital da Under-5 Health Center.

Idan ba a manta ba a shekaran bara ne Shugaban Kwamitin gudanarwa na hukumar inshorar lafiya ta kasa Enyanatu Ifenne ta bayyana cewa hukumar ta dakatar asibitoci 23 cikin 57 a kasar nan ci gaba da zama cikin shirin inshorar kiwon lafiya ta kasa.

Ifenne ta ce sun yi haka ne bayan jarabawar da suka gudanar wa duk asibitocin inda suka gano cewa asibitoci 34 ne kawai ke aiwatar da aiyukkan su yadda ya kamata.

” A jarabawar da muka yi wa asibitocin asibiti daya ne a duk fadin kasar nan ta sami maki 100 bisa 100.”

A dalilin haka ne hukumar ta dakatar da wadannan asibitocin ci gaba da Zama cikin shirin inshorar lafiya domin sabawa dokar gudanar da aiyukkan da shirin ya gindaya.

Share.

game da Author