Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa cutar yoyon fitsari cuta ce dake cutar da lafiyar mata wanda idan ba a gaggauta daukan mataki ba ya kan yi ajalin mace.
Ya fadi haka ne a taron wayar da kan mutane game da yadda cutar ke illata mata da aka yi a Abuja a makon da ya gabata.
Ya ce hakan na yiwuwa ne idan mace ta sami doguwar nakuda ko kuma idan shekarun haihuwan mace basu isa ta fara haihuwa ba sannan ta haihu ba tare da samun kulan kwararru ba a lokacin da suke haihuwa.
Ya bayyana cewa an fi samun wannan matsalane a yankin arewacin Najeriya.
Bincike ya nuna a shekara akan sami matan da suke fama da wannan cutar da suka kai 12,000 zuwa 15,000.
‘‘Sanadiyyar wannan cutar matan dake fama da wannan cutar na zama cikin kadaici da tabuwan hankali saboda kaurace musu da ‘yan uwa, abokanai da mazajen su ke yi.”
Adewole yace koda yake ana iya warkewa daga cutar ta hanyar yin aiki, ya kamata a rika bari yara na yin kwari kafin ayi musus aure sannan a rika ganin likita a duk lokacin da ake kokarin haihuwa.
Ya ce domi rage mace macen mata gwamnati ta hada hannu da wata kungiya mai zaman kanta ‘Engender Health/Fistula Care Plus’ domin yi wa matan dake fama da wannan cutar fida.
” Daga yanzu asibitocin gwamnati dake kasar na za su fara yin fidar wannan cutar sannan ita wannan kungiya za ta samar wa asibitocin da kayan aiki.
Adewole yayi kira ga shugabannin unguwanni, sarakuna, malaman addini da su yawaita yi wa mata wa’azi da fadakarwa game da yadda zasu kiyaye kansu.