Tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa Allah ba zai yafe masa ba idan har ya mara wa tsohon mataimakin sa Atiku Abubakar baya a 2019.
Obasanjo ya ce bai rasa wanda zai mara wa baya ba da za ace wai shi ne da kan sa zai mara wa Atiku baya a 2019.
“Idan kaga nayi haka to bada sani na bane amma idan har ko da sani na ne bazan taba mara masa baya ba.
” Ni fa da kuke gani na dinnan bana gaba da kowa a kasar nan. Idan kaga na fara gaba da kai toh, ba ka kauna da kishin Najeriya ne. Ni kuwa duk wanda baya kauna da kishin Najeriya da talakawan Najeriya bana tare da shi. Amma idan kana kaunar wannan kasar to muna tare tamau.
” Na fa san Atiku kamar yunwan ciki na. Kuma matsayi na a kan sa bai canza ba. Idan ya’ya na zasu yi aure yana aiko da wakilan sa haka nima idan nasa za su yi ina aikawa da nawa wakilan. Amma wannan dabam, ba siyasa ba ne.
” Idan da na mara masa baya a lokacin da ban san shi ba, yan zu ba zan yi haka ba domin na san shi kamar yunwan ciki na. Ba zan mara masa baya ba a siyasan ce ba.
Obasanjo da Atiku sun dade suna kai ruwa rana a fagen siyasar Najeriya. Duk da kuwa sun yi aiki ne tare a wancan lokaci, Obasanjo bai yarda da takun Atiku a siyasar Najeriya ba, yana mai cewa tun a wancan lokacin Atiku ba abin amincewa da bane.
Ko alokaci Obasanj yayi kokari canza shi amma bai yiwu ba, haka dai suka ganganda suka kari sa mulkin tare.
Obasanjo ya bayyana haka ne a filin jirgin saman Abuja, bayan dawowa da yayi daga kigal, kasar Kongo.