Anya Shehu Sani ya yi shawarar Arziki kuwa, Daga Hassana Yunus

0

Masu bibiyar siyasar jihar Kaduna sun rufta cikin duhu matuka sun kasa gane wacce irin siyasa ce Sanata dake wakiltar Kaduna ta tsakiya Shehu Sani yake yi.

A gani na na mai bibiyar siyasa a jihar Kaduna, ban ga alaman akwai lissafi a cikin shawarar da Shehu Sani ya ke kokarin dauka ko ya dauka ba.

Tun bayan darewar gwamnatin jihar Kaduna sanata Shehu Sani suka saka kafar wando daya da gwamnan jihar Nasiru El-Rufai.

Ya kai ga zagin uwa da uba ne kawai ‘yan siyasan basu yi wa juna. Amma duk kalaman batanci sun yi wa juna.

Kai ga har tsinuwa an yiyyi-yi duk saboda ba a samu yadda ake so.

Kowa ya san Shehu Sani da zama dan gaban goshin shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da ake ganin da zarar ya ce ga inda ya dosa duk za su bi shi sai gashi ana ta rade-radin cewa ya na lallabar gwamnatin jihar da ta yi yafe masa a sasan ta.

Masu yin nazari a siyasar jihar Kaduna, sun bayyana karara cewa hakan ba zai taba yiwuwa ba sai dai idan ba gwamna El-Rufai bane ke gwamnan jihar Kaduna.

El-Rufai ya nemi bashi da ga bankin duniya, kuma wannan banki ta amince masa amma sai da amincewar majalisar dattawa, da Shehu Sani ne ke shugabantar kwamitin da ke kula da karbo basukka daga kasashen waje.

Shehu Sani ya yi mursisi tare da sauran sanatocin jihar suka ki amincewa da a baiwa jihar Kaduna wannan bashi.

Ya sha fitowa yana nuna su fa sun kusa yar da kwallon mangwaro su rabu da kuda sai kuma gashi shi har yanzu yana tsotse wannan mangwaro.

Ina ganin sanata Shehu Sani ya kamata ya farfado daga wannan barci da yake yi ya gane cewa siyasa da ban take da gwagwarmaya, Idan ka shiga siyasa to alkiblar gwagwarmayarka zai canza domin sai ka fada cikin kamayamaya irin ta siyasa.

Idan ko haka ne toh dole ka zabi daya. A yadda abubuwa suke gudana yanzu, abin da kamar wuya. Ace wai akwai wani tasiri da za ka iya yi a siyasa muddun a jihar Kaduna za ka buga ta kuma a jam’iyyar APC.

A na haka ne kuma a makon da muke ciki jam’iyyar APC a jihar Kaduna ta sanar cewa Shehu Sani na nan a matsayin korarre a jam’iyyar APC.

Wasu na cewa kila balaguron siyasar sa a nan za ta tsaya, baya muradin ci gaba da ita kuma.

Ina ganin a jefar da wannan mangwaro haka na a tsallako tekun baharmaliya tunda shi kan sa Musa ma ya tsallaka, sannan Fir’auna ya dulmuye tun-tuni.

Share.

game da Author