Idan ba a manta ba siyasar Najeriya ta canza salo a cikin makonni biyu da suka gabata. Inda aka yi ta samun ficewar wasu gaggan ‘yan siyasar da suka hada karfi da karfe suka kafa gwamnatin jam’iyyar APC a 2015.
A kowani lokaci idan siyasa ta kunno kai akan samu irin wannan canje-canje ga ‘yan siyasa musamman wadanda ba su ji dadin gwamnatin da ke mulki a wannan lokaci ba.
Sau da yawa zaka ga karti na ta zabga musu, kai har hammata akan ba iska idan har ba jam’iyyar APC kake muradi ba, amma kuma sai dai a kiyasin masu yin fashin baki a harkar siyasar Najeriya sun lissafa cewa kusan kashi 75 na wadanda suke APC suna jam’iyyar ne don gujewa EFCC, wato su sami kariya daga gwamnati kuma amba su.
A wani musu da naji wasu nayi wani cewa yayi idan fa kana APC kai waliyi ne Idan ko ka ki yin ta, ka zama Fir’auna”
Da gwamnoni da Sanatoci, da ‘yan majalisa duk canza sheka suka yi amma dukiyoyin su da abubuwan da suke takama da su duk a mulkin PDP suka wawuro su.
Idan kana APC kai waliyi ne Idan Ka fita kazama Fir’auna
Abin da ke daure wa mutane da dama kai a siyasar Najeriya shine ganin yadda musamman a yanzu ake ganin idan har baka muradin jam’iyyar APC wasu sai su ga kamar sabo kayi, kila ma wani ya soke ka da sai ka kara yin kalmar shahada.
Ita jam’iyyar APC dai jam’iyyu ne suka hadu suka dunkule wuri daya suka kafa ta. Gaggan ‘yan jam’iyyar PDP da ake yi wa kallon hadarin kaji yanzu don sun fice daga jam’iyyar su na daga cikin wadanda suka fi kowa kashe dukiyoyin su wajen kamfen din 2015.
Ba za a manta da irin gudunmuwar da shugaban majalisar dattawa na yanzu Bukola Saraki ya bada ba a wancan lokaci, Babbar laifin sa shine zama shugaban Majalisar dattawa. Tun daga wannan lokaci ta inda ake shiga ba tanan ake fita ba game da al-a murran sa.
Magoya bayan APC a ko-ina- ba su ganin laifin ka idan dai jam’iyyar APC kake yi. Ko wacce irin laifi ka aikata kuwa lasisin zaman lafiyar ka shine ka yi nutso a jam’iyyar APC, idan kayi haka kasha. Haka duk magoya bayan APC suke lissafin su.
A lokacin da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, Kakakin majalisa Aminu Tambuwal, Bukola Saraki, suka canza sheka suka koma jam’iyyar APC, babu irin bukin da ba a yi ba don nuna murnar shigowar su jam’iyyar, a lokacin sun zama waliyyai an yi musu wankan tsarki amma kuma yanzu sun zama abin kyama tunda sun koma inda suka fito duk da irin gudunmuwar da suka bada a wancan lokacin har zuwa yanzu.
Tsakanin Tambuwal Da Wammako
Idan ka na bibiyyar yadda siyasar Sokoto ke gudana zaka gane cewa jam’iyya ba ita bace a gaban mutanen Sokoto, ayyukan ka a matsayin gwamna ne zai fidda kai daga jin kunya.
An yi mummunar adawa tsakanin tsofoffin gwamanonin jihar a shekarun baya. Ba za a manta irin gudunmuwa da ci gaba da Attahiru Bafarawa ya kawo jihar Sokoto ba, amma yadda kasan jefar da tsohuwar tsumma bashi da wuya haka aka yi masa da Aliyu Wamakko ya zama gwamna a jihar.
Yanzu dai an ja daga tsakanin sanata Wamakko da Gwamna Aminu Tambuwal. Wamakko ya ragargaji gwamnan inda ya kira shi matashi da bai iya siyasa ba, kawai don ya fice daga APC, amma kuma yana jinjina masa a lokacin da yake PDP domin shi kan sa a jam’iyyar ce ya kwankwadi romon kujerar gwamna da ya rike a wancan lokaci.
Yanzu dai goguwar canza jam’iyya ya kunno kai, sai dai a wannan karon idan ka canza ka zama fir’auna.