AMBALIYA: Ruwan sama ya yi barna a garin Dambatta

0

Wani ruwan sama mai karfi da aka sheka har tsawon awa hudu, ya kashe mutum daya, kuma ya lalata gidaje 40 a garin Dambatta, cikin jihar Kano.

Ruwan wanda aka ce an fara sheka shi tunn karfe 4:30 na yamma, ya kai awa hudu kafin ya dauke.

Kan silan Karamar Hukumar mai wakiltar mazabar Dambatta ta Gabas, Abdullahi Dambatta, shi ne ya bayyana haka ranar Juma’a a Kano, ga Kamfanin Dillancin Labarai, NAN.

Ya ce mutum daya ya rasa ran sa sanadiyyar gini da ya fado masa a Unguwar Makafi.

Ya kara da ewa unguwannin da ruwan ya yi barna, sun hada Bakin Kasuwa da kuma Mayanka duk a cikin Dambatta.

Shugaban Karamar Hukumar Dambatta, Idris Zago ya kai ziyarar jajentawa a yankunan da ta’adin ruwan ya shafa, domin ya tantane iyar barnar da ruwan ya yi.

Kan silan ya e jama’a da dama sun rasa wurinn kwanciya sanadiyyar wannan ambaliya.

Sakataren Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Kano, Ali Bashir, ya tabbatar wa faruwar amfaliya, ya kuma kara da cewa jami’an sa sun tafi domin su tantane irin barnar da ruwan ya yi.

Shi kuma kansilan ya roki shugaban karamar hukuma da gwamnatinn jihar Kano a kai daukin gaggawa ga al’ummar da abin ya shafa.

Share.

game da Author