Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Mahmood Yakubu, ya shigar da daukaka kara inda ya ke kalubalantar umarnin kama shi da Mai Shari’a na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yi.
A cikin karar da ya daukaka, Yakubu ya na kalubalantar sahihanci da cancantar umarnin kamun da alkalin Babbar Kotun Tarayya ya ce a yi masa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Babban Lauyan nan Adegbeoyega Awomolo (SAN), ya shigar da karar a madadin sa a yau Alhamis, a Abuja.
Shugaban na INEC ya ce bai yiwuwa haka kawai a zo a kama shi a bisa hujjar umarnin da aka bayar wanda umarnin raunana ne a idon shari’a.
Daga nan sai ya roki Babbar Kotun Daukaka Kara da ta yi amfani da karfin ikon da ta ke da shi, ta soke umarnin kamun da aka ce wa a yi masa, wanda mai shari’a Stephen Pam ya bayar.
Pam ya bada bada umarnin a kamo masa shugaban na INEC a gabatar da shi a gaban kotu, a ranar 8 Ga Agusta, domin a tuhume shi da kin bin umarnin kiran da kotu ta yi masa.
An bayar da wannan umarni ne saboda Yakubu ya ki zuwa kotu dangane da wata kara da jam’iyyar PDP reshen jihar Anambra ta shigar.
An nemi ya je kotun ranar 5 da kuma 10 Ga Yuli, amma bai je ba.
Wannan ne ya sa Babbar Kotun ta nemi ya je ya yi bayanin dalilin da zai sa a ki tura shi kurkuku, saboda kin amincewa da PDP bangaren Oguebego, kamar yadda Kotun Koli ta zartas.
Sai dai kuma shugaban na INEC ya musanta kin bin umarnin kotu, ya na mai cewa an yi masa rashin adalcin kin jin ta bakin sa da kotun ta yi.
Daga nan ya kara da ewa babu wata hujjar da ke nuna cewa an kai ko an aika ko an ba shi sammacen kai kan sa kotu ba.
Daga nan sai ya nuna kotun ta tafka kuskure a bisa doka da har ta bayar da umarnin a kama shi.
Sai ya roki kotun ta bayyana cewa babu wasu dalilai gamsassu da kotun za ta bayar na dalilin bada umarni kama shi.
Discussion about this post