Za a kara wa mata hutun shayarwa a Najeriya – Inji Ministan Lafiya

0

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa ma’aikatar sa za ta hada hannu da ma’aikatar kwadago domin a kara yawan kwanakin hutu da ake ba mata idan suka zo haihuwa a kasar nan musamman masu aiki.

Ya ce burin sa shine a kara yawan kwanakin daga watanni hudu zuwa watanni shida domin hakan zai taimaka wajen ba mata isasshen lokaci domin shayar da ‘ya’yan su nono yadda ya kamata.

Ya fadi haka ne a taron tattauna mahimmancin shayar da yara nonon uwa da aka yi a Abuja wannan mako.

Adewole yace ka’ida ne mace ta shayar da danta nono zalla na watanni shida kafin a fara bashi abinci domin hakan na taimaka wa wajen inganta lafiyar yaro kafin nan kuma yana da kyau a ci gaba da shayar da yaron har na tsawon shekaru biyu.

” Da yake mata basu samun lokaci su shayar da ‘ya’yan su ana samun yawan mace macen yara a kasan. Bincike ya nuna cewa kashi 17 bisa 100 ne kacal ke samun shayarwar uwa a kasar nan.

Ya ce hakan na da nasaba ne da rashin samun isasshen hutun da ya kamata uwa ta samu da kuma wasu matsaloli kamar haka.

Adewole ya ce domin shawo kan wadannan matsaloli ne ma’aikatar sa ke kokarin ganin gwamnati ta kara wa mata yawan hutu.

A karshe jami’ar UNICEF Pernille Ironside ta yaba wa ma’aikatan.

Share.

game da Author