Jam’iyyar APC a jihar Kaduna ta bayyana cewa sanatan da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, korarre ne a Jam’iyyar a jihar har yanzu fa.
Wannan ya biyo bayan wata sanarwa ne da ‘yan jam’iyyar na mazabar sanatan da ke Tudun Wada Kaduna cewa sanata Shehu Sani korarrene a Jam’iyyar har yanzu.
Sai dai kuma a farkon bayanin da shugaban jam’iyyar APC na jihar Kaduna Emmanuel Jekada ya fitar ya ce ba shi da masaniya kan wannan takarda da mazabar Sanata Shehu Sani suka fitar, domin irin wannnan takarda dole sai ya biyo ta ofishin sa kuma shi bai gan ta ba.
Jekada ya ce babu wannan magana domin ko a yanzu haka ya kafa kwamiti domin dinke barakar da ya dabaibaye jam’iyyar a jihar.
Shima Sanata Shehu Sani a martani da ya maida ya wa jam’iyyar ya bayyana cewa babu maganar dakatar da shi da a ke cewa anyi a Jam’iyyar kamar yadda ake ta yayadawa.
Ya ce wannan zancen kanzon kurege ne domin kuwa ba abin bi ko yarda dashi bane.
Ya ce yananan a dan APC dinsa kuma cikakken dan jam’iyya.