Shugaba Muhammadu Buhari ya misalta masu ficewa daga APC a matsayin baragurbi, ko kuma kwai da ake kira dakwaye, wadanda ya ce “Allah zai ci gaba da fallasa su daya bayan daya ya na fid da su daga cikin mu.”
Buhari ya yi wannan furucin ne a Bauchi, yayin da ya ke jawabi ga dimbin magoya bayan APC, wadanda ya ce kada ma su damu da wadanda ke ficewa daga APC.
Buhari wanda tuni ya daure kayan sa ya na shirin tafiya hutun kwanaki goma a Landan, ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya je taya dan takarar jam’iyyar APC na zaben cike-gurbin sanatan Bauchi ta Kudu, wato Gumau Yahaya.
Za a yi zaben ne a ranar 11 Ga Agusta, 2018.
Wata takardar manema labarai da aka fitar daga ofishin shugaba Buhari, ta ce gwamnatin APC tsaye ta ke daram, kuma za ta ci gaba da cika alkawurran ayyukan da ta yi wa jama’a alkawari domin inganta tattalin arzikin kasa da kuma kawo tsaro a kasar nan, tare da hana cin hanci da rashawa.
A kan haka ne Buhari ya ce a irin yadda ya gano lagon kasar nan, ba zai taba bari a cuci al’umma ba.
Wadanda suka raka Buhari a wurin kamfen a Bauchi, sun hada da Shugaban Jam’iyyar APC, Adams, Oshimhole, Gwamnonin Bauchi, Filato, Kano da Imo da wasu manyan shugabannin jam’iyyar APC.
Buhari ya ce ya amince da Gumau Yahaya kuma ya roki jama’a su zabe shi a matsayin sabon sanatan yankin Bauchi ta Kudu.
Daga nan ya gode wa al’ummar Bauchi saboda irin karba hannu bibbiyu da aka yi masa.