Ficewar shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki daga jam’iyyar APC zuwa PDP na neman tada wata dadaddiyar kiyayya a ciki-cikin gidan Saraki.
Bukola Saraki da kanwarsa Gbemisola Saraki sun fantsama kogin gaba a harkokin siyasa tun a shekarar 2011.
Bayanai sun nuna cewa Bukoka da Gbemisola sun fara kiyayya da juna ne tun bayan Bukola ya ki amincewa wa kanwar sa Gbemisola ta fito takarar gwamna na jihar Kwara a 2011.
Bukola ya tsaya fatatau cewa Gbemi ba za ta yi gwamna ba a jihar da hakan ya sa mahaifin sa ya fusata a kai a wancan lokaci.
Bayan nan Gbemi ta fice daga jam’iyyar PDP ta koma APC domin ma ta yi nesa da wan nata, wato Bukola. Jim kadan bayan haka shima Bukola ya fice daga jam’iyyar PDP ya koma APC.
Bukola bayyana haka ne a shafin sa na tiwita ranar Talata, ya na mai cewa ya dauki wannan shawara ne bayan zurfin tunani da ganawa da yayi da makusantar sa da abokanan siyasar sa.
A jam’iyyar APC ne Bukola ya zama shugaban majalisar dattawa, da hakan bai yi wa wasu jigajigan jam’iyyar dadi ba da har ka kwashe tsawon shekaru 3 na ta zaman doya da manja a tsakanin fannin zartaswa da bangaren majalisa.
Ranar Talatar da ta gabata kuwa ya fito ya ce gara ya yadda kwallon mangwaro ko ya rabu da kuda, ya bayyana canza shekar sa daga APC zuwa PDP.
Ita kuwa Kanwar sa, Gbemisola ta bayyana cewa yanzu ne ma taga ta zama a jam’iyyar APC, dama bata so suna jam’iyya daya da wan nata ba.
Gbemisola a shafin sada zuntar ta Facebook ta sanar cewa ta na nan daram a jam’iyyar APC kuma zata yi aiki da tabbatar da ganin jihar Kwara ta ci gaba da zama a jam’iyyar APC.
” Ina mai tabbatar muku da cewa nan ba da dadewa ba kungiyoyina na GRS Movement, GRS Friends on facebook, Paramount Women Forum (PWF),GRS Grassroots Youth Movements (GRS-GYM) da gidauniyata na GRS za mu fara aikin nema wa Buhari da jam’iyyar APC kuri’uwanda nayi ma taken “Get-Out-The-Vote” for PMB and APC.”
Ta ce abin da za ta maida hankali a kai kenan da ga yanzu har zuwa lokacin zabe.