Rundunar’yan sandan jihar Filato ta sanar cewa mutane biyar sun rasa rayukan su a sabuwar rikici da ya barke a jihar.
Kakakin rundunar Terna Tyopev ya sanar da haka ranar Laraba a garin Jos inda ya kara da cewa an yi rikicin ne a garin Rafiki dake titin Rukuba a garin Jos.
Kafin mu isa wannan wuri wadanda suka kai wannan hari duk sun gudu a cewar kakakin ‘yan sanda.
” Da muka isa wannan wuri sai muka tadda gawar mutane hudu, harsashen da aka yi amfani da su da kuma tabar wiwi da kwalaben giya.
Ya tabbata cewa rikici ne tsakanin wasu ‘yan kungiyar asiri, da rikici ya kaure a tsakanin su.
Ya kuma ce sun aika da jami’an tsaro wannan Unguwan domin ganin an sami tabbatacciyar zaman lafiya.
Wani mazaunin unguwan Rafiki Audu Kogi mahaifin daya daga cikin mutane hudu din da aka kashe ya ce wasu makiyaya ne suka far wa matasan dake zaune a wata ‘yar bukka suna hutawa bayn sun dawo daga daji.
” A dan kwanankin baya mazauna wannan gari sun gargadi makiyaya da ke bi ta gonakin su da su dai na haka, amma suka ki sai daga baya suka aika wa matasan unguwan sakon cewa sunanan dawowa.
” Mai unguwan kauyen da sauran mutane sun kasa daukan mataki domin babu wanda ya san ranar da wadannan makiyaya za su dawo sai ko ga su ko sun dawo ranar Talata kuma suka aikata wannan mummunar abu.
Wadanda suka rasu sun hada da Moses Aruku, Lucky Kogi, Ifeanyi Mbanafo da wani Sunday.
Sannan wani Ishaya da Paye sun sami rauni a harin.
Discussion about this post