Babu abin da APC ta rasa daga ficewar Saraki – Lai Mohammed

0

Gwamnatin Najeriya ta maida martani dangane da canjin shekar daga Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, daga APC zuwa PDP.

Gwamnati ta ce ai ficewar Saraki wani nauyi ne aka sauke wa jam’iyyar APC, dama ya zama karfen-kafa, kuma alakakai ga jam’iyyar.

Haka nan kuma gwamnatin ta ce Saraki a ko yaushe ya na adawa da jam’iyyar APC duk kuwa da cewa a cikin ta ya ke kafin ya fice.

Da ya ke magana, Ministan Yada Labarai Lai Mohammed, ya kara da cewa Saraki ya rika yin amfani da mukamin sa na Shugaban Majalisar Dattawa ya na yi wa gwamnatin Najeriya kafar-ungulu.

Lai ya bayyana haka ne ga manema labarai na fadar gwamnatin tarayya, jimkadan bayan tashi daga taron mako-mako na Majalisar Zartaswa tare da Shugaba Muhammadu Buhari.

Lai ya kara da cewa dama can tun da farko ana tababar cikar Saraki dan jam’iyyar APC tammi.

“Ba na jin gwamnati ta taba shan wahalar neman a sakar mata kasafin kudi kamar lokacin shugabancin Saraki a Majalisar Dattawa. Haka ya rika yin halayyar sa kai ka ce dan adawa ne, ba dan jam’iyya mai mulki ba.

Ministan ya kara da cewa babu abin da APC ta rasa daga ficewar Saraki. Da shi da babu, duk daya.

Share.

game da Author