Cutar ‘Diabetes’ da a ke kira ciwon siga ya kasu kashi daban-daban ne amma bayanai sun nuna cewa an fi kamuwa da wanda ake kira ‘Type -2 diabetes’.
” Kiba, shan taba, shan giya, yawan shan kayan zaki, rashin motsa jiki da makamantan su na daga cikin abubuwa da ke sa a kamu da wannan cuta.
Masana wannan cuta sun bayyana cewa a dalilin kamuwa da ita mutum kan iya makancewa, kamuwa da cutar koda, shanyewar bangaren jiki hawan jini da sauran su.
” Bincike ya nuna cewa a shekarar 2015 cutar ta yi ajalin mutane sama da miliyan 1.6 a duniya.”
Bayan haka wata sabuwar bincike da wasu likitoci suka yi a kasar Canada ya nuna cewa a kwai hadari idan mai dauke da cutar siga musamman ‘Type -2 diabetes’ ya canza irin maganin da yake sha zuwa ba tare da izinin likita ba.
Likitocin sun ce ka’ida ne mai dauke da cutar ya yi amfani da maganin ‘Metformin’ amma yanzu mutane sun fara zumudin canza maganin da suke sha zuwa wata sabuwan maganin mai suna ‘Sulfonylureas’.
” Sakamakon binciken da muka gudanar ya nuna cewa maganin Sulfonylureas na da ingancin rage adadin yawan sigan dake jikin mutum amma yana cutar da lafiyar masu dauke da cutar domin yakan haddasa cutar zuciya da wasu damuwa da akan yi ajalin mai dauke da su.”
A karshe likitocin sun ce kamata ya yi duk mai dauke da cutar siga ya ya gana da likitan sa kafin ya canza magani