Asusun samar da tallafi wa kananan yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta bayyana cewa bincike ya nuna cewa a duk awa daya matasa 30 ne ‘yan shekaru 10 zuwa 19 suke kamuwa da cutar kanjamau.
UNICEF ta ce hakan na da nasaba da talauci, rashin sani game da cutar, saduwa tsakanin na mace da na miji da wurwuri da dai sauran su na sa hakan na faruwa.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne kungiyar raya kasashe na kasar Amurka (UNAIDS) ta bayyana cewa an sami karin sabbin mutane har miliyan 1.8 da suka kamu da cutar kanjamau a duniya.
UNAIDS ta ce an sami wannan karuwa ne a dalilin rashin maida hankali wajen kawar da cutar da ‘yan siyasa ke nunawa, rashin wayar da kan mutane game da cutar da kin bin hanyoyin gujewa kamuwa da ita.
” Bisa ga binciken da muka gudanar bayanai sun nuna cewa kashe 47 bisa 100 na karuwai da masu shan miyagun kwayoyi na cikin mutanen da suka fi kamuwa da cutar. Sannan matasa mata da maza akalla 6,500 a duniya na kamuwa da cutar kanjamau duk mako.
A karshe UNAIDS da UNICEF sun ce kamata ya yi gwamnatocin duniya su gane cewa hakin su ne kare kiwon lafiyar mutanen kasashen su sannan su zage damtse wajen samar da isassun magunguna, wayar da kan mutanen musamman matasa kuma su samar da hanyoyin samun kariya daga cutar.
Discussion about this post