Jam’iyyar APC ta bayyana cewa ficewar shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da gwamnonin jam’iyyar APC biyu da suka yi bai dada jam’iyyar da kasa ba ko kadan.
Jam’iyyar APC jam’iyya ce da ta ba duk wani dan ta damar zama a cikin ta ko kuma idan yaga ba zai iya ba ya kakkabe nasa-ina-sa ya kara gaba.
” Mu dai muna ma kowa fatan alkhairi, sannan muna kira ga magoya bayan mu a wadannan jihohi da su ci gaba da yi wa jam’iyyar aiki da mara mata baya.
A safiyar Laraba gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar APC zuwa PDP.
Tambuwal tare da wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin jihar ne suka canza shekar.
Sai dai kuma, wasu daga cikin su sun fito sun bayyana cewa basu cikin wadanda suka fice daga jam’iyyar APC tare da Tambuwal din.
Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya bayyana ficewar sa daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.
Tambuwal, wanda ake da yakinin ya na da muradin takarar Shugabancin Kasa, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da kuri’un su, su fitar da Shugaba Muhammadu Buhari daga mulki.
Ya ce Buhari bai iya rike ragamar mulki yadda ya kamata ba.
Tambuwal ya ce ya yanke shawarar ficewa daga APC, saboda Buhari ya kasa yin abin da aka yi tsammani zai yi wa Najeriya. Don haka abin da ya fi kawai shi ne a kawar da shi zaben 2019 kawai.
Tambuwal ya bar PDP ne a cikin watan Afrilu, 2014, ya koma APC shi da wasu gwamnoni da Bukola Saraki da kuma Atiku Abubakar.
Discussion about this post