Wasu daga ciki ‘Yan majalisar Jihar Sokoto 12 sun ki bin gwamnan jihar komawa jam’iyyar PDP.
‘Yan majalisar sun ce sun gamsu da ayyukan da Buhari ke yi wa ‘yan NAjeriya sannan tare da shi da Jam’iyyar APC 100 bisa 100.
Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya bayyana ficewar sa daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.
Tambuwal, wanda ake da yakinin ya na da muradin takarar Shugabancin Kasa, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da kuri’un su, su fitar da Shugaba Muhammadu Buhari daga mulki.
Ya ce Buhari bai iya rike ragamar mulki yadda ya kamata ba.
Tambuwal ya ce ya yanke shawarar ficewa daga APC, saboda Buhari ya kasa yin abin da aka yi tsammani zai yi wa Najeriya. Don haka abin da ya fi kawai shi ne a kawar da shi zaben 2019 kawai.
Tambuwal ya bar PDP ne a cikin watan Afrilu, 2014, ya koma APC shi da wasu gwamnoni da Bukola Saraki da kuma Atiku Abubakar.

Tambuwal aboki ne na kut-da-kut ga Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, wanda ake wa kallon babban jigon PDP a halin yanzu.
Idan ba a manta ba a jiya Talata ne shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar APC tare da gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed.
Sannan bayan haka kuma a safiyar Laraban yau, kakakin jam’iyyar APC Bolaji Abdullahi da yan majalisar dokoki na jihar Kwara kaf din su suka sanar da ficewa daga jam’iyyar APC din.
Kada a manta shima jakadan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu, Musa Ibeto, ya mika takardar Ajiye aikin sa na jakadanci ya fice daga jam’iyyar APC din zuwa PDP.
Bayan haka tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar yayi maraba da dawowar shugaban Majalisar dattawa Bukola Saraki jam’iyyar PDP.
Atiku ya bayyana haka a sakon taya murna da nuna farincikin sa ga Saraki da dawowa jam’iyyar PDP.
Atiku ya ce Saraki mutum ne da dole a jinjina wa ganin irin gudunmuwar da ya baiwa jam’iyyar APC.
Ya ce jam’iyyar PDP na yi masa maraba.