Shehu Sani ya ba Buhari da masu ficewa daga APC shawara

0

Sanata Shehu Sani wanda ke wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya, ya shawarci gwamnatin tarayya dangane da hanyoyin da za ta bi ta samu zaman lafiya da masu ficewa daga jam’iyyar APC.

Shehu Sani ya shiga shafin san a Facebook ya yi wani bayani dalla-dalla, a safiyar yau Laraba, inda ya bayar da shawarar yadda za a ci gaba da mu’amala da juna, domin samun gudanar da ayyukan gwamnati zuwa karshen wannan zangon mulki, wato Mayu, 2019.

SHAWARWARIN SANATA SHEHU SANI

Tilas sai bangarorin biyu sun cire son kai, sun sa kishin kasa a farkon komai.

2. Bangaren Gudanarwa (Shugaban Kasa da Ministoci) su kasance su girmama wadanda suka fice daga APC, su ci gaba da kyakkyawar hulda da su, kuma kada su kuskura a rika yi musu bi-ta-da-kullin musgunawa saboda wasu dalilai na siyasa.

3. Majalisar Dattawa da a yanzu ke karkashin masu adawa, kada ta yi amfani da rinjayen adawar da ta ke da shi a majalisa ta rika kawo wa bangaren ayyukan gwamnati cikas da tsaiko. Sannan kuma su sani, Shugaban Kasa a matsayin sa na shugaba, tilas a ba shi girman sa da kuma kimar ofishin da ya ke rike.

4. A daina duk wasu surutai da hayaniya da kalaman batanci a tsakanin juna da gaggawa.

5. Tilas bangarorin biyu su maida hankali wajen ganin an magance mummunar matsalar tsaro da kasar nan ke fama da ita. Sannan kuma bayar da matukar gudummawar ganin an gudanar da zaben 2019 cikin nasara.

Share.

game da Author