Tuhume-Tuhume 7 da APC ke bukatar Saraki ya amsa nan da awa 48

0

Jam’iyyar APC ta gudanar da taron gaggawa sa’o’i kadan bayan Saraki ya yi sanarwar ficewar sa daga jam’iyyar ya koma PDP in da suka nemi ya qanke kansa kan wasu tuhume-tuhume 7 ko jam’iyyar ta hukunta shi.

1 – Kai ne kanwa-uwar-gamin kulla kutunguilar ficewar Sanatoci daga jam’iyyar APC zuwa wasu jam’iyyun adawa.

2 – Kiri-kiri ka ki zaman tantance sunayen wasu da Shugaba Muhammadu Buhari ya nada a kan wasu mukamai, wadanda kuma ‘yan jam’iyyar APC ne. Wannan ya jefa APC cikin matukar jin kunya, kuma tozartawa ce ka yi wa gwamnatin APC.

3 – Ka je jihar ka, ka shirya gangami inda magoya bayan ka suka nemi ka fice daga APC ka koma PDP. Bayan wannan ganganmi da ka yi, sai shi kuma Gwamnan Jihar Kwara, wanda dama dan gaban goshin ka ne, shi ma ya fito ya yi sanarwar cewa wa’adin kwanakin sa cikin APC sun kusa cika. Wannan ya nuna cewa kun nuna ficewar za ku yi.

4 – Ka yi amfani da ofishin Shugaban Majalisar Dattawa ka haifar da tsaiko da jinkiri na ba gaira ba dalili ga kasafin kudi. Wannan ya kawo jinkirin aiwatar da wasu ayyukan raya kasa wadanda ke cikin kudirorin da jam’iyyar APC ta yi wa jama’a alkawarin za ta samar musu idan ta kafa gwamnati, tun can baya da ta na kamfen.

5 – Ka rika yin amfani da Gidan Saukar Baki na Shugaban Majalisar Dattawa, ka na gudanar da tarukan yi wa jam’iyya zagon-kasa a ciki. A ciki ne ma ka tattara sunayen wadanda suka fice daga jam’iyyar APC.

6 – Ka karbi wasikar da gungun wadanda suka fice daga APC suka rubuta, kai kuma ka karanta a cikin zauren majalisa a bainar jama’a, cikin har ka ambaci sunan wanda bai kai ga cewa ya fice daga APC ba. Wannan ya tozarta jam’iyya matuka.

7 – Duk da irin kokarin sasantawar da aka rika yi da masu korafe-korafe, amma sai ka bijire ta rika tara hasalallun cikin jam’iyya, kai ne har da kafa wata kungiyar bijirarrun cikin jam’iyya.”

Share.

game da Author