Zan magance Boko Haram, kuma na kara hada kan Najeriya – Atiku

0

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya ce idan har aka zabe shi ya zama shugaban kasa, zai magance matsalar Boko Haram, sannan kuma ya kara hada kan kasar nan.

Ya kara da cewa idan da shi ne kan mukamin da Buhari ya ke a yanzu, da tuni ya kori Shugabannin Hukumomin Tsaron Kasar nan kakaf, saboda kowa dai ya san sun kasa magance Boko Haram a cikin shekarun nan sama da uku da gwamnatin Buhari ta yi.

Atiku yayi wannan jawabi ne a Maiduguri, babban birnin jihar Barno, ya na kuma mai karawa da cewa bai gamsu da yadda Buhari ke yi wa matsalar Boko Haram rikon sakainar kashi ba.

Atiku ya je Maiduguri ne da nufin yawo hankalin wakilan jam’iyya domin idan zaben fidda gwanin dan takarar PDP na shugaban kasa ya zo, su jefa masa kuri’a.

Ya yi taron ganawa da wakilan jam’iyyar PDP na jihohin Barno da Yobe.

Daga nan sai kuma ya jajanta wa al’ummar jihohin biyu dangane da dimbin asarar rayukan da suka yi saboda bala’in Boko Haram.

Ya ce matsalar tsaro a kasar nan ita ce zai fara sawa a gaba idan har ya zama shugaban kasa a zaben 2019.

Ya kuma yi alkawarin cewa al’ummar jihohin Barno da Yobe za su amfana sosai daga gwamnatin sa idan ya ci zabe a 2019, kasancewa tun daga 1999 har zuwa yau yankin duk a sahun baya aka bar shi wajen ci gaban kasa.

Share.

game da Author