Zan kori ministan Buhari daga APC idan yaki bin Umarni na – Adams Oshiomhole

0

Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole ya bayyana wa manema labari a fadar shugaban kasa cewa ya gargadi ministan Kwadago da ya tabbata ya bi umarnin sa ko ya kore shi daga jam’iyyar kai tsaye.

Oshimhole ya ce dole ne fa ko wani dan jam’iyya ya yi wa jam’iyya biyayya.

Oshiomhole da minista Chris Ngige sun sa kafar wando daya ne tun bayan umartar sa da yayi na ya yi maza-maza ya rantsar da kwamitin hukumomin gwamnati da ke karkashin ma’aikatar kwadago da aka nada amma har yanzu ba a yi ba.

Ko da yake Minista Ngige ya bayyana cewa ya rantsar da uku daga cikin kwamitocin da aka nada, amma kuma sauran ana dan bincike ne akai tukuna.

” Babu yadda za ayi ace wai kana minista kuma wai ba za ka rika nuna dattaku da yin abin da ya kamata ba. A sani babu wanda ya fi karfin jam’iyya.

” Idan shugaban kasa ya na iya daukar wargi, ni fa ba zan dauki haka ba musamman a abubuwan da ya shafi jam’iyyar mu. Sannan idan muka kori ministan za mu tabbatar cewa shi kansa shugaban kasa bai ci gaba da aiki da shi ba.

Oshiomhole ya ce kawai wadannan mutane suna amfadi da saukin kan Buhrai domin yin abin da suka ga dama. Yace wannan damar ya kare a karkashin shugabancin sa.

” Saboda haka ba za mu bari suna cin karen su babu babbaka ba, suna sakala sunar shugaban kasa a abubuwan da bai ma sani ba suna yin abin da suka dama. Su karya doka wajen bada kwangiloli sannan suna yi kamar su shafaffu ne da mai.

” Yanzu kowa ya sani, dole kabi yadda shugaban kasa ya umurce ka kayi, sannan kabi dokar jam’iyya ko kuma mu kora can ka je kayi mulkin ka a wata gwamnatin amma ba tamu mai adalci ba.

” Idan fa suna ganin sun yi abin da suka ga dama a da, yanzu an sake lale, duk wanda ya yi za a yi masa, zamu kore daga jam’iyya sannan mutabbata ba ka cikin gwamnati ko kai waye.

Share.

game da Author