Ba kamar yadda mutane musamman ‘yan siyasa suke tunani ba cewa Fayose zai taka rawar gani a zaben jihar Ekiti da ya gudana wajen tabbatar da ko ta halin kaka sai dan takarar jam’iyyar sa ta PDP ya lashe zaben gwamnan jihar.
Abin dai ya zama tarihi yanzu domin kuwa an gwada karfi tsakani jam’iyyun biyu a jihar sannan ‘yan takarar biyu duk sun fafata, sai dai kash sakamakon zaben ya ba da PDP domin kuwa cikin kananan hukumomi 16, APC ta lashe 12 ita kuma PDP ta cinye sauran hudun.
Idan ba a manta ba tun a shekarar 2016 tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose ya ke kurin wai shi cikakken dan tasha ne, wanda gaba daya babu sako ko lungun da bai sani ba a jihar Ekiti, sannan kuma bashi da wata sana’a da wuce siyasa.
” Allah ya kai mu 2018, zan nuna wa Fayemi na APC cewa shi ba dan tasha ba ne. Nine a garin Ekiti kuma bani da sana’ar da ta wuce siyasa. Yadda kasan Dutse haka nike, ka dake ni ka karairaye in dake ka ka rugurguje. Haka zan yi wa APC.” Inji Fayose Kafin Zabe
Sai dai kuma duk da cika bakin da yayi sai gashi ko karamar hukumar sa ya kasa ci.
Bayan haka jam’iyyar PDP ta ce tana ganawa a tsakanin mambobin ta sannan za ta fitar da matsayar ta game da sakamakon Zaben.
APC ta lashe zaben da Kuri’u 197,459 daga kananan hukumomi 12 da ya lashe ita kuma PDP ta samu kuri’u 178,121.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon taya Fayemi murnar lashe zaben da yayi sannan ya jinjina wa hukumar zabe gane da yadda ta suka gudanar da zaben a jihar.